Connect with us

Labaran Kano

Gwamnatin Kano ta haɗe Ma’aikatar Ruwa Muhalli da Sauyin Yanayi zuwa ma’aikata guda

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da haɗe Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi zuwa ma’aikata guda ɗaya mai suna Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi. 

Gwamnatin ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin da take yi na inganta gudanar da ayyuka da kuma haɗa ƙarfi wajen magance batutuwan da suka shafi ruwa, muhalli da sauyin yanayi a jihar.

A wata sanarwa da Kwamishinan sabuwar Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir M. Hashim ya fitar, ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya amince da haɗe ma’aikatun biyu tare da naɗa shi a matsayin wanda zai jagoranci sabuwar ma’aikatar.

Dakta Dahir Hashim ya bayyana cewa shi da tawagarsa sun shirya tsaf domin tabbatar da sauyin ya gudana cikin nasara, tare da ƙarfafa ayyukan da suka shafi kula da muhalli, yaƙi da illolin sauyin yanayi da kuma inganta sarrafa albarkatun ruwa domin amfanin al’ummar Jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!