Manyan Labarai
An gano wanda ya fito a bidiyon da ake zargin Daurawa ne
Wani mutum mai suna Ibrahim Muhammad Jidda mazaunin garin Maiduguri ya bayyana cewa bidiyon nan da ake yadawa kan cewa Sheikh Aminu Daurawa ne ke tikar rawa a wurin taron biki ba gaskiya bane.
A cewar Ibrahim Muhammad Jidda cikin wani faifan sauti da ya saki a shafukan sada zumunta, a ala-hakika ba shi bane domin kuwa lamarin ya faru ne akan idon sa a wani dakin taro mai suna White Arena dake GRA a Maidugurin.
‘Yace mutumin da aka nuno a cikin bidiyon kani ne ga wani dan siyasa a Maiduguri da ya samu halartar bikin, amma sam ba Mallam Daurawa bane sai dai sunyi kama sosai da Mallam Daurawa din.
Saurari cikakken bayanin nasa a kasa:
Tun da farko dai an fara yada wannan bidiyo ne wanda ke nuna wani mutum da wata suna tikar rawa a wurin taron biki inda aka rika yada shi da sunan cewa wai Mallam Daurawa ne ke waccen rawar.
Kalli wasu bayanai da aka wallafa a shafin facebook kan bidiyon a kasa.
Sai dai tuni Shehin malamin ya fito ya karyata labarin.
Rubutu masu alaka:
An gano wanda ya fito a bidiyon da ake zargin Daurawa ne
Za’a sanyawa unguwannin ‘yan gayu na’ura mai amfani da hasken rana