Connect with us

Labarai

A ƙara haƙuri kan aikin titin Kano zuwa Abuja – Buhari

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya aiko tawaga ta musamman domin tattaunawa kan aikin titin Kano zuwa Abuja.

Tawagar na bisa jagorancin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Farfesa Ibrahim Gambari.

Yayin duba aikin a jihar Kaduna Gambari ya ce, duba da muhimmancin da aikin, ya sanya shugaban ƙasa ya turo ayarin domin duba yadda aikin ke tafiya.

A cewarsa, matsalar da turakun wuta na cikin abin da ke kawo tsaiko a aikin.

Saboda haka ya roƙi al’umma su ci gaba haƙuri har zuwa kammala aikin.

Hoto a yayin taron.

A jawabinsa Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce, ya bayyana gamsuwarsa kan yadda aikin ke gudana.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayin da ya ke jawabi a wurin taron.

Daga cikin waɗanda ke cikin tawagar sun haɗa da, ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola.

Da kuma ministar kuɗi Zainab Shamsuna Ahmad.

Labarai masu alaka:

Shamsu Kura ya kalubalanci Buhari kan aikin titin Kano zuwa Abuja

Ƴan majalisa na duba ayyukan gwamnatin tarayya a Kano

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,910 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!