Labarai
A sanya dokar gwaji kafin aure – masu Sikila
Kungiyar masu fama da cutar sikila a Kano sun nemi gwamnati ta kafa dokar tilasta gwajin jini kafin aure.
Kungiyar ta ce ta hakan ne za a samu nasarar magance yawan masu fama da lalurar sikila a Najeriya.
Shugabar kungiyar, Rukayya Kamal Ibrahim yayin shirin barka da Hantsi na Freedom Rediyo da ya mayar da hankali kan ranar masu lalurar sikila ta duniya, ta ce masu fama da wannan ciwo na cikin mawuyacin hali, don haka akwai bukatar gwamnatoci su tashi tsaye domin shawo kan matsalar.
“Ya kamata gwamnatin Kano da ma Najeriya ta samar da asibitoci na musamman da zasu rika kula da masu cutar sikila, musamman a bangaren basu agajin gaggawa, domin a halin yanzu shine babbar matsalar da muka fama da ita” inji Rukayya Kamal.
You must be logged in to post a comment Login