Labarai
Hatsarin dake tattare da wallafa hotuna a shafukan sada zumunta
Wani al’amari da ke faruwa a yanzu bai wuce dauke-dauken hotuna da wasu mutane ke yi lokacin da wani iftila’i ya faru ba, musamman hatsari ko gobara ko rushewar gini, inda suke sanyawa a shafukan sada zumunta na intanet ds makamantansu.
Wannan dabi’a ta jima tana ciwa mutane tuwo a kwarya kasancewar wanda iftila’i ya faru da shi ya fi bukatar agajin gaggawa ba wai daukar hotonsa ana yayatawa ba.
Wannan al’amari dai ya jima yana faruwa a cikin mutane, inda masu ikata hakan ke mayar da hanakali dajen daukar hotunan maimakon bada agajin gaggawa ga wadanda hatsarin ya ritsa da su.
Kasancewar dabi’ar ta zama ruwan dare a wannan zamani, dalilin kenan da ya sanya a ‘yan kwanankin nan hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta kasa tare da hadin gwiwar wata kungiya mai zaman kanta suka koka game da halayyar daukar hoto ko bidiyo idan aka samu hatsari.
Batutuwa masu nasaba
Citad: bude shafukan boge da sunan shugabanni na kara yada kalaman batanci
Muhimman abubuwan da suka faru a Kannywood cikin makon da ya gabata
Abunda ya kamata ku sani kan Tasirin yada labarun karya yake
Kun san dalilan da suka sanya aka garkame Sadiya Haruna a gidan yari?
Shugaban hukumar kiyaye aukuwar hadurran ta kasa Mr Hyginus Omeje ne ya bayyana hakan yayin taron da wata kungiya mai rajin bayar da gudunmawa kan harkokin lafiya ta shirya.
Freedom Radio ta zanta da wasu mutane a nan Kano, inda suka bayyana wannan mummunar dabi’a a matsayin abin takaici.
Amma sun nemi hukumomi su dauki matakin da ya dace don kauda barna.
Yayin zantawarsa da Freedom Radio shugaban kungiyar bada agajin gaggawa ta kasa reshen jihar Kano Musa Danladi Abdullahi, ya ce wanda iftila’i ya fadawa, to babu abinda ya fi bukata da ya wuce agajin gaggawa, a don haka ma kungiyar ta su ke bada horo ga matasa wajen nuna musu muhimmancin taimakawa al’umma a duk lokacin da wani iftila’i ya same su.
Kabir Ibrahim Daura shi ne jami’in hulda da jama’a na hukumar kare aukuwar hadurra ta kasa shiyyar Kano jan hankalin jama’a ya yi da su kaucewa wannan dabi’a.
Ya kuma kara da cewa suna wayar da kan mutane wajen sanin muhimmancin taimakawa al’umma idan har sun samu hatsari, ba wai daukar hoto ko bidiyo ba, a watsa a shafukan sada zumunta ba.
Wasu daga cikin mutane na da dabi’ar daukar hoto da zarar an yi hatsari ko wani iftila’I idan ya afku.