Connect with us

KannyWood

Abinda ya sanya ba zan iya auren Yawale a zahiri ba -Rayya

Published

on

Abinda ya sanya ba zan iya auren Yawale a zahiri ba -Rayya

Jarumar wasan kwaikwayon nan Surayya Aminu wadda akafi sa ni da Rayya a shirin film din Kwana Casa’in ta bayyana cewa ita fa a zahiri ba zata iya auren abokin wasanta Yawale ba, domin kuwa Yawalen yana da mata, ita kuma ba ta son kishiya, sannan kuma ba shi da kudi alhalin ita kuma mai kudi take so.

Acikin wata tattaunawa da Rayyan ta yi da Freedom Radio ta ce “Yawale abokin aikina ne, Yawale yana da mata ni kuma bana son kishiya, amma da ace ma bashi da mata, ni nafi karfin Yawale, don bashi da kudi, ni kuma mai kudi nake nema”.

Saurari tattaunawar Rayyan.

Sai dai bayan da Freedom Radio ta sanya wannan tattaunawa acikin shirin ta na Indaranka a kwanakin baya, jarumar ta fito ta janye wannan magana da tayi a shafinta na Instagram kamar yadda zaku ji a jawabinta dake kasa.

Rubutu mai alaka:

Yadda akayi auren mutu’a a Kannywood

Abinda yasa ‘yansanda suka cafke Sadiya Haruna

Kun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,669 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!