Labarai
Benue: Jami’an tsaro sun kubutar da daliban da aka sace a hanyar zuwa jarrabawar JAMB

Jami’an tsaro sun yi nasarar kubutar da daliban da aka sace a hanyar zuwa jarrabawar JAMB da sauran fasinjojin a Jihar Benue.
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar, Ifeanyi Emenari ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin da yake gabatar da mutane 15 daga cikin waɗanda aka ceto ga Gwamna Hyacinth Alia a fadar gwamnati da ke Makurdi.
Ya ce an samu nasarar ceto mutanen ne bayan wani samame na haɗin gwiwar jami’an tsaro, kuma duka mutanen suna cikin ƙoshin lafiya.
Kwamishinan ya kuma sanar da kama mutane bakwai da ake zargi da hannu a lamarin, yana mai bayyana hakan a matsayin babban ci gaba a binciken da ake yi.
You must be logged in to post a comment Login