Coronavirus
Adadin masu Corona sun haura 100 a jihar Borno
Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da cewa yanzu haka mutane 106 aka tabbatar sun kamu da cutar Covid-19 a jihar.
Ma’aikatar lafiya ta jihar Borno ta wallafa a shafinta na Twitter cewa a ranar Talata an samu karin mutane 6 wadanda suka kamu da cutar a jihar, wanda ya kai adadin zuwa mutane 106.
As at 11:40pm 5th, May, 2020. @NCDCgov confirmed new 6 cases of Covid19 in Borno state.
Total confirmed cases: 106
Active cases: 90
Discharged: 2
Deaths: 14 pic.twitter.com/St6fgALH91— Borno State Ministry Of Health And Human Services (@Borno_Health) May 6, 2020
Har ila yau, sanarwar ta kara da cewa izuwa yanzu mutane 14 ne suka rasa ransu sanadiyyar cutar a jihar.
Wakilin mu a jihar Borno Alaji Ibrahim Injiniya ya zanta da kwamishinan lafiya na jihar Dakta Salihu Aliyu Kwaya-Bura wanda ya tabbatar masa da cewa yanzu an sallami mutane 2 na farko da suka warke daga cutar Covid-19 a jihar.
Karin Labarai:
Ma’aikatan lafiya 7 sun kamu da Coronavirus a Borno
Rundunar Soji ta musanta labarin kai hari barikin sojoji a Borno
You must be logged in to post a comment Login