Labaran Wasanni
AFN Crisis: Kowane shugaban tsagin bangarorin biyu zai gudanar da zabensa da ban
Rikicin shugancin hukumar wasannin guje-guje da tsalla-tsalle ta kasa AFN, na kara kamari yayin da kowane tsagin bangarorin biyu ke shirin gudanar da zabe a yau Litinin 14 ga watan Yuni.
Yayin da masu ruwa da tsaki a hukumar dake goyon bayan shugaban daya bangaren Inginiya Ibrahim Shehu Gusau za su gudanar da zabensu a jihar Kebbi.
Haka kuma, suma daya tsagin bangaren da shugaba Hon. Olamide George ke jagoranta dake samun goyon bayan ma’aikatar wasanni ta kasa za su gudanar da nasu zaben a Abuja.
A kwanakin baya ne hukumar wasan gudu da tsalle-tsalle ta duniya tare da mambobin hukumar AFN suka gudanar da taron kwanaki biyu don yin sasanci tsakanin bangarorin biyu, inda aka cimma matsayar gudanar da zabe a ranar 14 ga watan Yuni a yunkurin kawo karshen rikicin.
Yanzu haka dai masu ruwa da tsaki na cigaba da sanya ido domin ganin yadda sakamakon zaben guda biyu za su kasance.
AMM
You must be logged in to post a comment Login