Labarai
Akwai yiwuwar Ganduje ya ‘karawa ‘yan kasuwa ranakun sararawa
Gwamnatin Kano ta ce zata karawa ‘yan kasuwa kwana guda matukar sun bi dokar da aka gindaya musu kan Covid-19.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce matsawar ‘yan kasuwar suka bawa gwamnati hadin kai shakka babu akwai yuwuwar a kara musu kwana gudan da suka nema tun farko.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da jagorancin tawagar masu feshin magani a kasuwar sabon gari da ke birnin Kano, a wani bangare na tunkarar cutar Coronavirus da ma sauran cutuka masu yaduwa a jihar.
“Fatan mu shine mu kakkabe annobar Covid-19 da ma sauran cutuka masu yaduwa a jiharmu, don haka muna bukatar goyon baya daga al’ummar jihar”. a cewar sa
Gwamnan ya kuma kara bawa al’ummar Kano hakurin zaman gida da suke yi, inda yace hakan wani mataki ne na dakile yaduwar annobar Covid-19 a tsakanin mutanen Kano.
You must be logged in to post a comment Login