Coronavirus
Almajirai 40 da Kano ta mayarwa da Jigawa na dauke da cutar Corona
Gwamnatin jihar Jigawa tace almajirai 40 daga cikin gwajin 145 da ya fito ya nuna suna dauke da cutar Covid-19.
Kwaminshinan lafiya na jihar Jigawa kuma shugaban kwamatin dakile yaduwar Covid-19 a jihar, Dr. Abba Umar Zakari ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo a birnin Dutse na jihar Jigawan.
Kwaminshinan yace daga cikin almajiran da jihar kano ta maidawa Jigawa sati biyu da suka wuce, sun dauki gwajin 600, wanda sakamakon guda 145 ya fito a yanzu kuma 40 daga ciki suna dauke da cutar.
Dr. Abba Ya ce sun kadu matuka da ganin sakamakon gwajin, wanda hakan shi ne ke nuna cewa akwai babban kalubale da ya ke bukatar ayi nazari mai zurfi.
Tuni dai aka fara raka almajiran da basa dauke da cutar zuwa garuruwan su, da tukwicin dinkin sallah da kuma kudi naira 10,000 ga kowanne, wanda a cewar kwamishinan gwamnan Jigawa Alh. Muhd Badaru Abubakar ya ne ya umar ce su da suyi haka.
Karin labarai:
Gwamna Badaru ya dinkawa Almajirai kayan sallah
Ma’aikatan lafiya sun kamu da Corona a Jigawa
Ya zuwa yanzu dai jihar Jigawa ta karbi almajirai ‘yan asalin jiharta sama da 1,000. daga jihohi daban-daban, da suka hada da Kano, Gombe, da Kaduna, sai kuma Nasarawa.
A wani bangaren kuma itama jihar Filato ana tsammanin yau zuwa Gobe zata angizo ayarin wasu almajirai yan asalin jihar ta Jigawa.
A wasu lokuta maban-banta Gwamna Badaru, ya bayyana cewa ba zai fitar da koda mutum guda daga jiharsa ba a cikin wannan yanayi na annoba.
You must be logged in to post a comment Login