Labarai
Ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita sassa da dama na ƙasar Senegal
Mummunar ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita sassa da dama na ƙasar Senegal biyo bayan mamakon ruwan sama da aka tafka a ƙarshen mako, wanda ya yi sanadin rayukan mutane da dama da jikkata wasu na daban, yayin da ƙasa da wata guda ya rage ƙasar ta karɓi baƙuncin gasar wasannin Olympics ta matasa.
Ma’aikatar Cikin Gida ta ƙasar ta tabbatar da cewa ambaliyar ta mamaye manyan hanyoyin mota, ta lalata gine-gine, sannan ta raba daruruwan iyalai da muhallansu, musamman a babban birnin ƙasar, Dakar, da sauran yankuna na karkara.
Hukumar kula da yanayi ta ƙasar ta bayyana cewa an auna adadin ruwan sama da ya kai milimita 142 a cikin sa’o’i 24 kacal a wasu yankunan, lamarin da ya sa magudanun ruwa suka kasa ɗaukar ambaliyar.
Rahotanni daga hukumomin agaji sun nuna cewa yawancin asarar rayukan sun auku ne sanadin ruftawar gine-gine da kuma ambaliyar da ta ratsa gidajen mutane ba zato ba tsammani, musamman a yankunan Parcelles Assainies da ke Dakar da kuma garin Kaolack.
Gwamnatin Senegal ta bayyana alhininta game da wannan barna, tana mai gargaɗin cewa ana iya fuskantar ƙarin ruwan sama a kwanaki masu zuwa.
You must be logged in to post a comment Login