Tsaro
Amurka ta kashe jagoran mayakan ISIS na duniya a Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce sojojin kasarsa sun yi nasarar hallaka Mataimakin Shugaban Ƙungiyar ISIS na duniya da ke ɓoye a Najeriya.
Trump ya ce sun samu nasarar kawar da Abu-Bilal al-Minuki a wani harin haɗin gwiwar dakarun ƙasarsa da na Najeriya suka kai a daren jiya Juma’a bayan samun bayanan sirri kan wurin da Abu Bilal yake ɓoye a Najeriya.
Trump ya bayyana haka ne a shafinsa na Truth Social inda ya bayyana cewa Abu Bilal Al-Munki bai san cewa Amurka na bibiyar sa kuma suna da majiyoyi da ke sanar da su duk halin da yake ciki ba.
You must be logged in to post a comment Login