Connect with us

Tsaro

‘Yan sanda sun fara bincike kan kisan Mata da Miji a jihar Kebbi

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta fara bincike da farautar wasu ‘yan bindiga da suka kashe wasu ma’aurata a kauyen Asarara da ke jihar Kebbi.

Kakakin rundunar a jihar, Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa an kai gawarwakin zuwa wani asibiti a Birnin Kebbi domin gudanar da bincike da gano wadanda suka aikata laifin.

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda aka kashe sun hada da Muhammad Haruna da matarsa Habiba Abubakar, inda aka ce an kai musu hari a gidansu da misalin karfe 5:30 na safiyar Asabar.

Wani mazaunin yankin ya bayyana marigayin Muhammad Haruna a matsayin mutum mai zaman lafiya wanda ba a san yana da wata rigima da kowa ba.

Lamarin ya jawo alhini a tsakanin al’ummar kauyen yayin da ma’auratan suka bar ‘ya’ya shida, maza hudu da mata biyu. ‘Yan sanda sun bukaci jama’a su bayar da duk wani bayani da zai taimaka wajen gano wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!