Labarai
Mahaifin Messi Jorge ya rasu yana da shekaru 68

Jorge Messi, mahaifin fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Argentina, Lionel Messi, ya rasu yana da shekaru 68 a birnin Rosario na ƙasar Argentina.
Rahotanni sun ce Jorge Messi ya rasu ne a daren Juma’a a wani asibiti, bayan shafe tsawon lokaci yana fama da rashin lafiya. Iyalansa ne suka tabbatar da rasuwar.
Jorge Messi ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar ɗansa, inda ya kasance wakilinsa tun lokacin da Lionel Messi yake matashi, tare da taimaka masa wajen tafiyar da harkokin ƙwallon ƙafa da kasuwancinsa.
Ya kuma kasance tare da Lionel Messi a lokacin da ya bar Argentina zuwa Barcelona yana ƙarami, inda wannan tafiya ta kasance farkon babbar hanyar da ta kai shi ga shahara a duniyar ƙwallon ƙafa.
You must be logged in to post a comment Login