Labaran Kano
An fara binciken ‘yan sandan da ake zargi da baiwa masu safarar kwayoyi gudummuwa
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta sauyawa baki dayan jami’anta dake aikin yaki da miyagun kwayoyi na hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro wurin aiki.
Kwamishinan ‘yan sandan na jihar Kano CP. Ahmed Iliyasu ne ya bada umarnin sauya musu wurin aikin, biyo bayan korafin da abokanan aikin su na hukumar KAROTA su ka yi na cewa idan suka kama kayan maye a yankin Sabon Gari dake nan Kano, sai su kuma ‘yan sandan su basu umarnin su sake shi.
Cikin wata tattaunawa da Freedom Radio tayi da kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwa al’amarin inda ya bayyana mana cewa baya ga sauyawa ‘yan sandan da ake zargi wurin aiki, tuni aka fara bincikar su kan lamarin domin daukar mataki bisa umarnin kwamishinan ‘yan sanda na jihar.
Allah ya kyauta.
RUBUTU MAI ALAKA:
‘Yansanda sun kama wani matashi mai garkuwa da mutane
Abinda yasa ‘yansanda suka cafke Sadiya Haruna
Yadda ‘Yansandan Kano suka cafke wadanda suka kone magidanci
Rundunar yan sandan Kano ta yi holin mutane 116 da ake zargi da manyan laifuka