Kiwon Lafiya
An fara rigakafin cutar amai da gudawa a Jigawa
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta fara gudanar da aikin rigakafin cutar kwalara a kananan hukumomi uku na jihar.
Babban sakataren hukumar bunkasa kiwon lafiya matakin farko na jihar, Dakta Kabiru Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da allurar rigakafin a kauyen Badanda, da ke karamar hukumar Dutse.
Ya ce Gwamnatin Tarayya ta ba da alluran rigakafin kusan miliyan 1 da dubu dari hudu da za a yi wa mutane daga shekara 1 zuwa sama.
Dr Kabiru ya yi bayanin cewa kimanin mutane 720 aka yi niyyar allurar rigakafi ta farko da ta biyu a Birnin Kudu, Dutse da Hadejia.
Ya ce manufar ita ce a takaita barkewar cutar kwalara da ta kashe daruruwan mutane a fadin jihar.
Don haka, ya bukaci mutane da su ba da hadin kai ga kokarin Gwamnati wajen dakile cutar.
You must be logged in to post a comment Login