Labaran Wasanni
An fitar da jerin sunayen ‘yan wasa 30 da za’a zabi gwarzon dan wasan Duniya
Mujallar wasanni ta kasar Faransa ta fitar da jerin ‘yan wasa 30 da acikinsu daya zai lashe kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2021.
Hukumar ta sanar da hakanne a ranar Juma’a 08 ga Oktoban shekarar 2021.
Cikin jerin ‘yan wasan dai akwai dan wasa Lionel Messi, Cristiano Ronaldo, Robert Lewandowski, Neymar, Karim Benzema, Jorginho N’Golo Kante na daga cikin ‘yan wasan da mujallar
Haka zalika suma ‘yan wasa Erling Haaland, Kylian Mbappe, Luka Modric, Phil Foden da Romelu Lukaku suma suna jikin jerin ‘yan wasan da ka iya lashe kyautar.
‘Yan jaridu daga kasashe daban-daban da masu horarwa da kyaftin-kyaftin ne dai suke gudanar da zaben domin samun wanda zai lashe kyautar ta Ballon d’O.
Bikin bada kyautar dai zai gudana a birnin Paris na kasar Faransa a ranar 29 ga Nuwamba mai kamawa.
Bikin bada kyautar Ballon d’Or dai bai gudana a shekarar 2020 sakamakon cutar Covid-19.
Dan wasa Messi dai shine ke rike da kambun kyautar bayan lashewa a shekarar 2019.
Yayin da dan wasan Bayern Munich Lewandowski bai samu damar lashewa ba, inda ya lashe kyautar gwarzan dan wasa FIFA.
Cikin jerin ‘yan wasa 30 da za suyi takarar lashe kyautar ta shekarar
2021 ta Ballon d’Or sun hada da…………..
Cesar Azpilicuerta
Nicolo Barella
Karim Benzema
Leonardo Bonucci
Giorgio Chiellini
Kevin De Bruyne
Ruben Dias
Gianluigi Donnarumma
Bruno Fernandes
Phil Foden
Erling Haaland
Jorginho
Harry Kane
N’Golo Kante
Simon Kjaer
Robert Lewandowski
Romelu Lukaku
Riyad Mahrez
Lautaro Martinez
Kylian Mbappe
Lionel Messi
Luka Modric
Gerard Moreno
Mason Mount
Neymar
Pedri
Cristiano Ronaldo
Mohamed Salah
Raheem Sterling
Luis Suarez
Kopa Trophy shortlist:
Mason Greenwood
Bukayo Saka Pedri,
Jeremy Doku, Ryan Gravenberch,
Jamal Musiala, Florian Wirtz,
Jude Bellingham, Giovanni Reyna,
Nuno Mendes.
You must be logged in to post a comment Login