Connect with us

KannyWood

An gano Jakadiyan Tona Asiri

Published

on

An gano Jakadiyan Tona Asiri

Cikin wani sautin muryar tattaunawar waya ta juramin fina-finan Hausa Isa A. Isa ya bayyana cewa jarumar nan da ta yi fice a shafukan sada zumunta wato Sadiya Haruna ta san wanene Jakadiyyan Tona Asiri kuma suna da alaka da ita.

Saurari tattaunawar ta Isa.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2019/10/Isa-Jakadiya_audio.mp3?_=1

Jakadiyyan Tona Asiri dai wani asusu (account) ne da ya jima a dandalin sada zumunta na Instagram wanda yake wallafa bayanan Gulma da Tsegumi musamman a masana’antar Kannywood, al’umma da dama dai na son ganin shin ko wacece ko waye wannan Jakadiya?

Tunda farko dai wani rikici ne ya barke a tsakanin Isan da kuma Sadiyar inda kowa ke kokarin tona asirin dan uwansa.

Ita ma a nata bangaren cikin wani sakon murya da ta aikewa Jakadiyar Tona Asiri, Sadiyar ta yi maganganu da suke gab da gasgata maganar Isan.

Saurari jawabin Sadiya.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2019/10/Sadiya-Jakadiya_audio.mp3?_=2

Izuwa yanzu dai tuni wannan batu ya fara daukar hazo a shafukan sada zumunta inda jama’a suke ta bayyana ra’ayoyi mabam-bamta akai.

Allah ya kyauta.

Rubutu mai alaka:

An fara sulhu tsakanin jaruman da suka yi auren mutu’a

An gano wanda ya fito a bidiyon da ake zargin Daurawa ne

Kun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!