Coronavirus
An hana mutane zuwa asibiti ba tare da “Face Mask” ba a Cross River
Gwamnatin jihar Cross River ta ce daga yanzu babu wanda zai shiga dukkan asibitocin dake jihar ba tare da takunkumin rufe baki da hanci ba.
Kwamishiniyar lafiya ta jihar kuma shugabar kwamitin kar ta kwana kan yaki da annobar Covid-19 Mrs. Betty Edu ce ta bayyana hakan a jiya Jumu’a yayin da ta kai ziyarar bazata babban asibitin garin Calabar.
Kwamishiniyar ta ce ganin yadda ake samun karuwar ma’aikatan lafiya dake kamuwa da cutar Covid-19 musamman a jihar Legas ya sanya tila su dauki wannan mataki domin kare lafiyar ma’aikatan lafiya.
Har ila yau, Mrs. Betty Edu ta ce a yanzu ya zama tilas ga marasa lafiya da ma’aikatan lafiyar da kuma masu zuwa asibitin su rika sanya takunkumin rufe baki da hanci, domin hakan zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar Covid-19.
Jaridar Premium Times ta rawaito cewa Kwamishiniyar ta rabawa ma’aikatan lafiya na babban asibitin garin Calabar kayayyakin kariya da sa su rika amfani da su a yayin gudanar da ayyukansu.
Har izuwa yanzu dai ba a samu rahoton bullar cutar Covid-19 a jibar ta Cross River ba.
You must be logged in to post a comment Login