Labarai
An horas da matasa dabarun wayar da kan mutane don ci gaba da ɗorewar zaman lafiya
Cibiyar bada horo kan ayyuka na musamman ta African Coaches Initiative horas da matasa a nan Kano kan hanyoyin tabbatar da zaman lafiya.
Yayin taron an horas da matasa kan dabarun wayar da kan mutane domin ci gaba da ɗorewar zaman lafiya.
Maryam Ado Haruna ita ce, jami’ar tsara shirin ta yi mana ƙarin haske kan taron.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da horon sun bayyana mana alfanin da irin wannan taruka ke yi musamman wajen wanzar da zaman lafiya.
Taron ya samu halartar matasa daga ƙungiyoyin al’umma da ƴan jarida da kuma jami’an hukumomin gwamnati.
You must be logged in to post a comment Login