Labarai
An karɓi sakamakon farko game da sabuwar cutar da ta ɓulla a Kano
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta yi ƙarin bayani kan sakamakon farko da ta samu daga birnin tarayya Abuja kan cutar da ta ɓulla a wasu yankunan Kano.
Babban jami’in kwamitin kar-ta-kwana mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa na ma’aikatar lafiya ta Kano Dr. Bashir Lawan ya ce, an samu fitowar sakamakon farko game da batun.
Wanda ya nuna cewa, ba zazzaɓin lassa ko cutar shawara ba ce.
Sannan sakamakon binciken ya nuna cewa, cutar ba ta da alaƙa da ruwan rijiyar da ke maƙabartar Ɗandolo.
Yanzu haka akwai sauran samfuri na sinadarin da ake haɗa lemo da sinadarin ɗan tsami wanda ake cigaba da bincike a kansa.
Kuma kawo yanzu an gano cewa, wa’adin amfani da sinadaran ya ƙare.
You must be logged in to post a comment Login