Manyan Labarai
An raba sinadarin wanke hannu a Asibitin Murtala
Shugaban kungiyar taimakon matasa ta Arewa, KuleChas Arewa kwamrade Abdullahi Aliyu ya yi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu dasu taimakawa gwamnati a kokarin da take na yakar cutar Corona.
Abdullahi Aliyu, yace kungiyoyi suna da rawar da zasu taka wajen taimakon al’umma ba sai gwamnati ka dai ba.
Abdullahi Aliyu ne ya bayyana haka lokacin da kungiyar su ta yi rabon kayan wanke hannu da tsafatar sa a asibitin Murtala.
Ya kara da cewa kungiyar su tana taimakawa asibiti da makarantun da kayan aiki kamar su sinadarin wanke hannu Sanitizer, domin yakar cutar Corona mai lakabin Covid 19.
Labarai masu alaka.
Dalilan da suka sanya Buk ta musanta bullar cutar Corona
Covid-19: An takaita zirga-zirga a kasuwar kantin Kwari
Yace sun kuma shirya bita don wayar da kan mutane akan cutar data gallabi al’ummar duniya dama kasa baki daya.
A nasa jawabin shugaban asibitin Murtala, Dakta Husaini Muhammad, ya yabawa wannan kungiya, tare da yi musu alkawarin hadin kai tsakanin Asibitin da kungiyar , tare da gode musu da bisa bada tallafin kayan wanke hannu.
Shamsu Dau Abdullahi, wakilin mu da ya halarci taron ya rawaito cewa marasa lafiya da dama ne suka samu wannan tallafi na kayan a kokarin da ake na dakile wannan cuta mai saurin hallaka mutane.
You must be logged in to post a comment Login