Jigawa
An rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar ICAN na Kano da Jigawa
Gwamatin jihar Jigawa ta yi kira ga sabbin shugabannin ƙungiyar akantoci ta ƙasa reshen jihar Kano da Jigawa (ICAN) da su yi aiki tuƙuru tare da fito da tsare-tsaren da za su ciyar da ƙungiyar gaba.
Mataimakin gwamnan jihar Alhaji Umar Namadi ne ya bayyana hakan yayin bikin rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar karo na talatin da tara da aka gudanar a nan jihar Kano.
Ya ƙara da cewa lokaci yayi da sabbin shugabannin za su mayar da hankali wajen wayar da kan ƴan kasuwa matsakaita da ƙanana don sanin muhimmancin ilimin akantanci tare da amfana dashi.
Namadi ya kuma yabawa ƙungiyar ta ICAN musamman wajen yadda take bai wa gwamnatoci shawara kan yadda za su magance matsalar tattalin arziki.
A nasa ɓangaren sabon shugaban ƙungiyar Dakta Abubakar Umar Farouk cewa yayi abin takaici ne yadda ake samun ƙarancin masu rubuta jarabawar zama ƙwararrun akantoci a ƙungiyar daga arewacin kasar nan.
Dakta Abubakar Umar ya kuma ce akwai mutanen da a shirye suke su ɗauki nauyin waɗanda za su rubuta jarabawar ƙungiyar sai dai rashin sani yasa da yawa al’ummar arewacin kasar nan na rasa damar.
You must be logged in to post a comment Login