Labarai
An rufe wasu cibiyoyin lafiya a Kano – Dakta Tijjani
Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wasu cibiyoyin lafiya 3 sakamakon kin sabunta rijstar su na shekarar 2020.
Wannan dai na cikin wata sanarwa da hukumar kula da lafiya da Cibiyoyin lafiya na jihar Kano ta fitar mai dauke da sa hannun sbabban sakataren hukumar Dakta Usman Tijjani Aliyu.
Sanarwar ta bayyana cewa an rufe cibiyoyin ne sakamakon rashin cika ka’idojin da hukumar ta sanya na sabubta rijisatarsu a kowacce shekarar.
A cewarsa asibitocin da aka rufe sun hadar da asibitin ido da ke kan titin Civic centre da asibitin hakori na Orbit da ke Sabon Titin Mandawari da asibitin hakori na ABC da ke kan titin zariya.
Dakta Tijjani Aliyu ya ce daga fara zagayen duban asibitin a farkon makon da muke ciki, hukumar ta rufe asibnitin Baraka da ke unguwar Darmanawa, da asibitin M. D. G. da ke hanyar Ribadu a karamar hukumar Tarauni.
A cewarsa matakin rufe su ya biyo bayan sabawa umarnin sabunta rijstar su da hukumar ta umarce su suyi duk shekarar, a don haka za a ci gaba da rufe wuraren har sai sun cika ka’ida.
You must be logged in to post a comment Login