Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

An yiwa mutane 19,512 gwajin cutar Corona a Najeriya

Published

on

Alkaluman cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC yace zuwa yanzu cibiyar ta yiwa mutane 19,512 gwajin cutar Covid-19 a sassa daban-daban na kasar.

A jadawalin bayanan cutar da cibiyar NCDC ta sanya a babban shafinta na Internet a ranar Laraba ya ce mutane 2,950 sakamakon gwajinsu ya nuna cewa suna dauke da cutar.

Har ila yau, kididdigar ta ce an sallami mutane 481 wadanda suka warke daga cutar.

Sannan mutane 98 sun rasa ransu sanadiyyar cutar ta Covid-19.

Har ila yau, Kididdigar ta NCDC tace yanzu haka masu dauke da cutar 2,371 ne suke karbar kulawar jami’an lafiya.

Karin labarai:

Wadanda suka warke daga Coronavirus a Najeriya sun doshi 500

Adadin masu Corona ya doshi 3,000 a Najeriya

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!