Labaran Kano
Ana zargin wani dan KAROTA da dabawa wasu direbobi wuka
Rikici ya rincabe tsakanin jami’an hukumar lura da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA da wasu direbobi a sha tale-talen gidan jaridar Triumph.
Sai dai rundunar ‘yan sandan Kano ta ce ana zargin daya daga cikin jami’an KAROTAn da cakawa direbobi biyu wuka.
Kakakin rundunar yan sandan jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce su na gudanar da bincike a kan al’amarin.
Freedom Radio ta yi kokarin jin ta bakin hukumar ta KAROTA domin jin matsayar ta akai, sai dai har zuwa wannan lokaci bamu samu ji daga gare su ba.
You must be logged in to post a comment Login