Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan bindinga sun sace mutane 15 a wani farmaki

Published

on

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki yankin Oluwalose dake Okolowo’n jihar Kwara, inda sukai awon gaba da mazauna yankin da daama.

Rahotannin sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar, sun yiwa kauyen ‘kawanya da tsakar daren jiya Talata tare da harbi kan mai uwa da wabi.

Wani mazaunin yankin ya tabbatarwa da Nigerian Tribune cewa, akalla mutane 15 aka sace, ciki har da shugaban al’ummar yankin Mista Buhari Tunde.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundinar ‘yan sandan jihar ya ce, suna kan kokarin yin duk mai yiyuwa wajen ganin a ceto su.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!