Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Magu: Osinbajo ya aikewa rundunar ‘yan sandan Najeriya wata wasika

Published

on

Mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya aika wasika ga Sufeto Janar na ‘yan sanda, Muhammed Adamu, kan zargin da ake masa na karbar wasu makudan kudade daga hannun shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu.

Wata jarida ta yanar gizo mai suna PointBlank News ta wallafa cewa akwai wasu kudade da suka kai naira biliyan talatin da tara da shugaban hukumar EFCCn ya kwato, inda ya bawa mataimakin shugaban na Najeriya Farfesa Osinbajo naira biliyan hudu a ciki.

Rahoton da jaridar ta wallafa ya ce sun samu wata majiya mai karfi daga fadar shugaban kasa kan cewa dakataccen shugaban hukumar EFCCn ya fallasa asirin mataimakin shugaban kasar a kan badakalar.

Tun farko a wata sanarwa da Farfesa Osinbajon ya fitar ta hannun kakakinsa, Laolu Akande, ya bayyana ikirarin a matsayin karya ce da bata da tushe.

Osinbajo a wata wasika da ya aikewa babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ta hannun lauyansa Taiwo Osipitan ya ce rahoton ba gaskiya bane illa yunkurin bata masa suna.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!