Coronavirus
Astrazeneca: Dakatar da rigakafin a wasu kasashen Turai zai sanya shakku ga Afirka – Dr. Richard
Shugaban aikin rigakafi na Hukumar lafiya ta Duniya WHO a Afirka, ya ce dakatar da amfani da rigakafin korona na Astrazeneca da kasashen Turai da dama suka yi, wani abin damuwa ne.
Kasashen Jamus da Faransa na cikin kasashen da suka dakatar da amfani da rigakafin na Oxford-Astrazeneca saboda fargabar yana da nasaba da daskarewar jini.
Dr Richard Mihigo ya ce har yanzu WHO na bayar da shawarar amfani da rigakafin, yana mai nuna damuwa cewa akwai yiwuwar gwiwar kasashen Afirka ta fara yin sanyi kan lamarin.
You must be logged in to post a comment Login