Ƙetare
Ba mu da niyyar cutar da Qatar- Majalisar tsaron Iran

Majalisar tsaron kasar Iran, ta ce, harin da ta kai sansanonin sojin Amurka da ke cikin Qatar ba shi da niyyar cutar da ƙasar.
Ta cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar, ta ce Iran za ta ci gaba da martaba dangantakar tarihin da ke tsakaninta da Qatar.
Harin baya ɗauke da wani hatsari ga mutanen Qatar, saboda ba ƙasar harin ya nufa ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa, yawan makamai masu linzamin da aka yi amfani da su a harin sun yi dai-dai da adadin boma-boman da Amurka ta yi amfani da su a cibiyoyin nukiliyar Iran uku.
Gwamnatin Qatar dai ta ce, na’urorin kakkaɓo makamanta sun samu nasarar daƙile makaman na Iran.
You must be logged in to post a comment Login