Siyasa
Babu abinda zai dakatar da shirin mu na zaben fidda gwaninn takarar shugaban kasa- PDP
Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce babu wani shiri na daban da zai dakatar da shirin ta na gudanar da zaben fidda gwanin da zai tsaya mata takarar shugabancin kasar nan a zaben shekara 2019 da zai gudana gobe Asabar a jihar Rivers
Jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar ta PDP Kola Ologbondiyan ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke zantawa da manema labarai kan sakamakon taron da kwamitin zartarwar jam’iyyar ya gudanar a jiya.
A cewar Ologbondiyan suna fatan za a gudanar da zaben cikin nasara da kuma lumana, maimakon kokarin da wasu kungiyoyi ke yi na shirya wata makarkashiya da za takawo cikas ga zaben da aka tsara gudanarwa a gobe Asabar a garin na Fatakwal.
Ya ce jam’iyyar tana sane da wadannan kalamai da yan adawa ke yi na cewar za a lalata zaben a don haka ne ya ce jam’iyyar ta shirya tsaf domin baiwa marar da kunya.
Inda ya ce uwar jam’iyyar ta samu rahoton cewa wasu kungiyoyi na yunkurin kawo cikas a zaben fidda gwanin domin ganin cewa jam’iyyar bata fitar da dan takara da zai tsaya mata a zabe mai zuwa ba.
Ologbondiyan ya ce sun gayyaci masu sanya ido daga kasashen ketare domin su shaida wannan makarkashiya da ake kullawa domin kawo cikas kan dan takarar da za su fitar da zai kara da shugaban kasa Muhammadu Buhari.