Addini
Babu laifi wajen yin ibadar da ba ta saba wa shari’a ba- Malamai
Wani malamin addini musulunci a jihar Kano ya bayyana cewa akwai abubuwa da yawa da basu inganta ba, sai dai kuma yin hakan idan har ya dace da bin Allah da manzonsa to ya na da kyau musulmi ya yi amfani da shi.
Limamin masallacin jumma’a na unguwar Rijyar Zaki, Malam Mukhtar Umar Sharada ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da Freedom Radio.
Malamin ya kara da cewa, idan har mutane suka tura sakonni musamman ma a kafar sadarwa suna cewa a lokaci kaza ana so a karanta kaza, ko ayi sallah raka’a kaza a lokacin azumi to ba laifi bane idan mutum yayi amfani da su a musulunce.
Domin jin ci gaban tattaunawar danna alamar Play.
You must be logged in to post a comment Login