Labarai
Ban sayar da otel din Daula ba – Ganduje
Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ake yadawa cewar ta sayarwa da dan kasuwar nan ma mallakin Mudassir and Brothers katafaren otal din Daula.
A tsakiyar makon nan ne labari ya fantsama cewar an sayar da wannan otal ga wannan ‘dan kasuwa, domin ya gina katafaren kantin komai da ruwanka a wannan wuri.
Gwamnatin Kano tace ko kadan babu batun sayar da wannan otal, amma yanzu haka gwamnati da wannan dan kasuwa sun fara kulla wata yarjejiniya domin inganta wannan wuri da nufin amfanar al’ummar jihar Kano.
Kwamishinan kudi na jihar Kano Hon Shehu Na’Allah kura ya shaidawa Freedom Radio cewar, otal din na Daula ya dauki shekaru cikin mummunan yanayi bayan watsi da gwamnatocin baya suka yi dashi, dan haka yace otal din ya lalace har takai ya fara zama barazana.
Karin labarai:
Bayan sauke Dan Sarauniya, Ganduje ya nada sabon kwamishina
Sati biyu kenan babu wanda ya rasu sanadiyyar Corona a Kano – Ganduje
Yace wannan ne ya sanya aka fara neman masu halin da zasu zuba jari don farfado dashi kuma a ka dauki lokaci ba a samu ba, saboda lalacewar da wurin yayi.
Don haka yace an bayar da wannan otal din ne, domin a yi abin da zai amfani al’ummar Kano kamar yadda aka yanka filin gwamnati aka bayar domin yin rukunin kantinan Ado Bayero Mall.
You must be logged in to post a comment Login