Labarai
Bangar siyasa na kawo koma baya ga matasa a tsakanin al’umma: Kungiya
- Kungiyar daliban hausawa ta Nijeriya shirya taron wayar da kan matasa kan illar shaye –shaye da bangar siyasa.
- Kungiyar ta bayyana hakan ne yayin wata zantawarta da Freedom Radio a safiyar yau Talata
- Kungiyar tayi kira ga matasa dasu dage wajen ganin sun zabi shuwagabanni na gari
Kungiyar daliban hausawa ta Nijeriya ta ce ta shirya taron wayar da kan matasa kan illar shaye –shaye da bangar siyasa a Kano ne don magance rigin –gimu a lokutan zabe shekarar da muke ciki ta 2023.
Sarkin daliban hausawan Najeriya Malam Nura Sulaiman Janburji ne ya bayyana hakan a zantawara sa da Freedom Radio a safiyar yau Talata.
Tattaunawar dai ta mayar da hankali ne kan taron wayar da kai da kungiyar ta shirya a Kanon.
Malam Nura Suleman Janburji ya kuma ce a lokacin taron za’a gabatar da bayanai daga malamai daban –daban, wadanda zasuyi tsokaci akan matsalolin da rigin-gimu a wurin zabe suke haifarwa al’umma.
Janburji yayi amfani da wannan damar wajan kira ga matasa dasu dage wajen ganin sun zabi shuwagabanni na gari, tare da gujewa yamutsi a lokacin zaben 2023.
Rahoton: Nura Bello
You must be logged in to post a comment Login