Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bangar siyasa na kawo koma baya ga matasa a tsakanin al’umma: Kungiya

Published

on

  • Kungiyar daliban hausawa ta Nijeriya shirya taron wayar da kan matasa kan illar shaye –shaye da bangar siyasa.
  • Kungiyar ta bayyana hakan ne yayin wata zantawarta da Freedom Radio a safiyar yau Talata
  • Kungiyar tayi kira ga matasa dasu dage wajen ganin sun zabi shuwagabanni na gari

Kungiyar daliban hausawa ta Nijeriya ta ce ta shirya taron wayar da kan matasa kan illar shaye –shaye da bangar siyasa a Kano ne don magance rigin –gimu a lokutan zabe shekarar da muke ciki ta 2023.

Sarkin daliban hausawan Najeriya Malam Nura Sulaiman Janburji ne ya bayyana hakan a zantawara sa da Freedom Radio a safiyar yau Talata.

Tattaunawar dai ta mayar da hankali ne kan taron wayar da kai da kungiyar ta shirya a Kanon.
Malam Nura Suleman Janburji ya kuma ce a lokacin taron za’a gabatar da bayanai daga malamai daban –daban, wadanda zasuyi tsokaci akan matsalolin da rigin-gimu a wurin zabe suke haifarwa al’umma.

Janburji yayi amfani da wannan damar wajan kira ga matasa dasu dage wajen ganin sun zabi shuwagabanni na gari, tare da gujewa yamutsi a lokacin zaben 2023.

Rahoton: Nura Bello

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!