Labaran Kano
Bayan ajiye aiki: Hadimi na musamman ga Ganduje ya fice daga jam’iyyar APC
Tsohon hadimi na musamman ga gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje Alhaji Sani Mohammed, wanda akafi sani da Sani Rogo ya bar jam’iyyar APC.
Rogo ya sanar da barin jam’iyyar APC ne ta cikin wasikar da ya aikewa shugaban jam’iyyar na mazabar Unguwa Uku cikin Gari, da ke yankin karamar hukumar Tarauni wadda ke dauke da kwanan watan 9 ga Disamban 2023.
Wata majiya ta tabbatarwa da Solasbase cewa, barin jam’iyyar da shahararren dan siyasar a karamar hukumar Tarauni yayi, na da nasaba da kama karya da ake masu cikin jam’iyar.
You must be logged in to post a comment Login