Labarai
Bayer Leverkusen ta zama Zakarar gasar Bundesliga ta bana
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024 bayan sa suka samu nasara kan Weder Bremen da ci 5-0.
Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich ta yi tana lashe gasar.
Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi.
Inda suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.
Kana a dai wannan shekara ne su ka yi rashin nasara hannun Shalke 04 a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.
Sannan Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.
Ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.
You must be logged in to post a comment Login