Ƙetare
Birtaniya ta sanya Nijeriya da kasashe 53 cikin jerin wadanda ta daina daukar ma’aikatan lafiya
Kasar Birtaniya ta sanya Najeriya da wasu kasashe 53, cikin jerin kasashen da ba za ta rika daukar ma’aikatan lafiya daga cikin su ba, bayan sauya ka’idojin daukar aiki a ma’aikatar lafiyar kasar.
Sanarwar da ke dauke da sabbin ka’idojin, ta shawarci hukumomin da cibiyoyin da ke daukar ma’aikatan lafiya su kiyaye kasashen da ke cikin wancan jeri a lokacin daukar ma’aikatan lafiya.
Wannan sabon tsarin dai ya shafi dukkanin ma’aikatan lafiya da za’a dauka aikin din-din-din da kuma na wucin gadi a Birtaniya, wanda ya shafi likitoci da Likitocin Hakori da jami’an kiwon lafiya da unguwar zoma da jami’an jinya da dai sauran su.
Idan dai za a iya tunawa a shekarar 2021 ne, kasar Birtaniya ta dakatar da daukar ma’aikatan lafiya daga Nijeriya da wasu kasashe 46, saboda barazanar kaura da kanana da matsakaitan kasashe ke fuskanta na karancin jami’an kiwon lafiya.
A ranar 8 ga watan Maris da ya gabata kuma hukumar lafiya ta duniya WHO ta lissafa Najeriya da wasu kasashe 54 da ke fuskantar karancin jami’an kiwon lafiya.
Rahotanni sun nuna cewar akwai kwararrun likitocin Najeriya dubu 11 da 55 da ke aiki a Ingila a yanzu haka, wanda hakan ya sanya kasar zama kasa ta uku da tafi yawan likitocin da ke aiki a kasar Ingila bayan India da Pakistan.
You must be logged in to post a comment Login