Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Black Friday: An samu saɓani tsakanin Hisbah da majalisar malamai a Kano

Published

on

Majalisar malamai ta jihar Kano ta ce, babu laifi cikin bikin ranar “Black Friday”.

Shugaban majalisar Malam Ibrahim Khalil ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.

Malam Khalil ya ce “Tun asali amfani da kalmar ‘Black Friday’ ba ya nufin mummunan abu, hassalima yabo ne”.

Ya ce “Ba magana ce ta suka ba, in ka kalli tarihi, sai dai in mutum bai binciki abin da faɗi ba”.

Labarai masu alaka:

Tallafin Corona: An dakatar da kwamandan Hisbah na Dala

Jami’an Hisbah sun karbi horo kan kokawar Karate a Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano dai ta aike da wasiƙa ga wasu manyan shagunan jihar, inda ta nemi dakatar da su daga bikin ranar.

Sannan ta aike makamanciyarta ga gidan rediyon Cool FM kan ya dakatar da shirye-shirye ko tallata ‘Black Friday’ ɗin.

Ko da muka tuntuɓi gidan rediyon na Cool mahukuntan sa sun ce kawo yanzu ba za su ce komai ba a kai.

Dangane da batun Hisbah Malam Khalil ya ce, bai san dalilin hukumar na ɗaukar waɗannan matakai ba, kuma indai da sunan addini ne to babu gaɓar kama wa.

Sheikh Khalil ya ce, laifin ƴan jarida ne da ba sa wayar da kan mutane game da irin waɗannan batutuwa.

Wasu cikin jami’an hukumar Hisbah na Kano.

Shi ma ɗaya daga cikin malaman addinin musulunci a Kano, Malam Abubakar Abdussalam Baban Gwale ya ce, bikin ranar halastacce ne.

Malamin ya ce “Batun wanda suka ƙirƙiri bikin ranar ko kiranta da ‘Black Friday’ ba za su sanya a haramta ta ba”.

A cewarsa “Shi yasa yawancin fatawar malamai ita ce, babu laifi mutum ya ci moriyar ranar ta hanyar sakko da farashin kayansa, ko kuma sayen kayayyaki, amma kada ya sayi haramtattun kaya”.

Karin labarai:

Aikin Allah: Ganduje zai yiwa ƴan Hisbah ƙarin albashi

Bama wuce gona da iri a ayyukan mu – Inji Hisbah

Masana shari’a dai sun soki lamirin hukumar Hisbar da cewa ya saɓa da doka.

Barista Abba Hikima Fagge lauya ne mai zama kansa a Kano.

Ya ce, “Idan aka duba sashi na 7 cikin dokar da ta kafa hukumar Hisba a shekarar 2003 ya nuna cewa aikinta shi ne, bai wa musulmi shawara”.

“Amma batun tilasta wa mutane ba su da wannan damar kwata-kwata a doka”.

Mun tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Hisbah Malam Ibrahim Lawan Fagge wanda ya ce, zai yi mana ƙarin bayani daga baya.

Kuma mun sake tuntuɓarsa bayan tsawon awanni amma ba mu same shi ba.

Mun kuma lalubi babban kwamandan hukumar Malam Haruna Ibn Sina ta wayar tarho amma bai ɗaga wayar ba.

Yanzu haka dai dubunnan al’umma ne ke ta bayyana ra’ayoyinsu a kai, musamman ma ta kafafen sada zumunta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!