Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya amince da kwangiloli 16 domin bunƙasa wutar lantarki

Published

on

Majalisar zartarwa ta ƙasa ta amince da bayar da kwangiloli 16 don farfaɗo da harkokin samar da wutar lantarki a Najeriya.
Majalisar ta amince da hakan a wani zama na musamman da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta yau a fadar shugaban ƙasa.

Yayin zaman an kuma amince da buƙatu guda 16 da ministan lantarki Injiniya Abubakar Aliyu ya gabatar wa majalisar.
Ministan ya ce, ƙarancin wutar lartarkin da ake samu a ƙasar nan na da alaƙa da yadda mahukunta suka yi watsi da ɓangaren a baya, ba tare da mayar da hankali wajen bunkasa shi ba yadda ya dace ba.

Ya ƙara da cewa ƙarancin wutar lantarki ya gurguntar da tattalin arziƙin ƙasar nan fiye da yadda ake zato.

Ƙarin labarai:

Za’a daga matsayin tashar wutar lantarki ta jihar Yobe

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!