Labarai
Buhari ya tashi tsaye wajen magance matsalar tsaro a Najeriya- Muryar Talaka
Wata kungiya da ke rajin kare hakkin marasa galihu mai suna ‘Muryar Talaka’, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya tashi tsaye don magance matsalar tsaro, musamman kashe-kashen babu gaira babu dalili da ke faruwa a arewacin kasar nan.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Balarabe Yusif Gajida.
Gwamnatin tarayya zata kasha naira biliyon goma wajen sayen maganin Kwari
Bamu bude shafin sayar da Form ba-NDA
Sanarwar ta ce, kungiyar ta damu matuka kan irin zubar da jinin al’umma da ke wakana a jihohin Katsina da Zamfara da Borno har ma da sauran jihohi da ke kasar nan.
A cewar kungiyar ta ‘Muryar Talata’ wajibi ne jami’an tsaro musamman sojoji da ‘yan sanda da kuma jami’an hukumar tsaron sirri ta DSS har ma gwamnonin arewacin kasar nan da su kara kaimi wajen ganin matsalar tsaro ta zamo tarihi a jihohin arewa.
You must be logged in to post a comment Login