Labaran Kano
Cakuda manya da kananan masu laifi bai dace ba – Kungiya
Wata kungiya a nan Kano mai suna Mu hadu mu gyara, ta bayyana damuwarta kan yadda ake cakuda masu manya da kananan laifi a wuri guda a gidajen gyaran hali, wanda hakan ke kara baiwa masu kananan laifin damar koyar munanan dabi’u da suka fi wanda suke aikatawa a baya muni.
Jami’in hulda da jama’a na biyu a kungiyar Malam Usman Abdullahi ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na nan tashar Freedom Radio da aka gudanar yau.
Malam Usman Abdullahi wanda ya ce kungiyar ta su ta hada gamayyar kungiyoyin ci gaban al’umma a jihar Kano, a don haka akwai bukatar hukumomi su duba matsalolin gidajen gyaran hali don magancesu.
Ya kara da cewa kamata ya yi matasa su kiyayi ba da damar yin amfani da su wajen bangar siyasa, sakamakon irin yadda ‘yan siyasar ke amfani da su ta hanyoyin da ba su kamata ba don cimma burinsu.
Barista Hannatu Adam Muhammad ta kungiyar kare hakkin dan adam da ci gaban al’umma, ta ce kungiyar su na daukar laifin fyade da muhimmanci, ta yadda suke tsananta bincike don tabbatar da kwatowa duk yarinyar da aka yi wa fyaden hakkinta.
Barista Hannatu ta bukaci iyaye mata su kara jan yaransu a jiki tare da nuna musu muhimmamcin bayyana damuwarsu ga iyaye, wanda hakan zai ba da dama wajen sanin halin da yaransu ke ciki a gida da waje.
You must be logged in to post a comment Login