Kiwon Lafiya
Cibiyar kare yaduwar cututtuka ta ce an samu raguwar cutar amai da gudawa
Cibiyar kare yaduwar cututtuka ta kasa ta ce an samu raguwar yaduwar cutar Amai da gudawa wato kwalara a kasar nan in banda wasu Jihohi 8 da har yanzu ake samun bullar cutar kadan.
Jihohin sune Adamawa da Bauchi da Kano da Katsina, sai Zamfara da Kogi da Plateau da kuma Kaduna.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa-hannun shugaban cibiyar Chikwe Ihekweazu, yana mai karin hasken cewa a cikin makwanni hudun da suka gabata babu batun bullar cutar a Jihohin Anambra da Nasarawa da kuma Yobe.
Mista Ihekweazu ya ce cibiyarsu na tallafawa Jihohin kasar nan wajen yakar cutar musamman ma inda aka rahoton bullarta.
Ya kuma kar da cewa kididdigar da su ke da ita ta nuna ya zuwa 8 ga watan Yulin nan da mu ke ciki sun samu rahoton bullar cutar sau 16,008 inda mutane 186 suka mutu a Jihohi 16 na kasar nan, tun daga farkon shekarar nan.
Haka zalika ya bayyana matakan kariya kan cutar da suka hadar da mayar da hankali wajen samar da ruwan sha mai tsafta ga al’umma, kasancewar rashinsa na haddasa cutar.