Labarai
Cire tallafin mai ya kara yawan masu zuba jari

Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar na taka muhimmiyar rawa wajen dawo da amincewar masu zuba jari a bangaren man fetur da iskar gas.
Shettima ya ce cire tallafin man fetur da sauye-sauyen kasuwar canjin kudaden waje sun taimaka wajen samar da yanayi mai kyau da zai ba ‘yan kasuwa damar zuba jari a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a Legas, yayin da ya kaddamar da sabon hedikwatar kamfanin Northwest Petroleum and Gas, inda ya ce bunkasar kamfanonin cikin gida na da muhimmanci wajen samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin Najeriya.
Mataimakin shugaban kasar ya kuma ce gwamnati za ta ci gaba da samar da yanayin da zai karfafa harkokin kasuwanci, kirkire-kirkire da ci gaban tattalin arziki.
You must be logged in to post a comment Login