Kiwon Lafiya
Yadda Coronavirus ta samo asali – Dr, Bashir Getso
Shugaban Kwalejin koyar da aikin tsafta ta Jihar Kano School of Hygiene Dakta Bashir Bala Getso, ya bayyana cewa cutar Corona ta samo asali ne daga haduwar wasu kwayoyin cututtuka masu raunana garkuwar jikin dan adam.
Dakta Bashir Bala Getso ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan tashar Freedom Radio, da ya tattauna kan yadda cutar ke kara yaduwa a kasar nan.
Ya ce cutar na farawa ne daga alamomin mura da sarkewar numfashi, sannan kuma idan har kwayar cutar ta fita daga jikin dan adam ta kan shafe tsawon mintuna talatin kafin ta mutu.
Dakta Bashir Bala Getso ya kara da cewa, cutar ba ta numfashi ake daukarta ba, tana kama dan adam ne ta hanyar taba wasu sassan jiki da hannun da ke dauke kwayoyin cutar.
Ya kuma daukar matakan kare yaduwar ne kadai zai taimaka wajen dakile ta, kamar yadda aka gani a kasar China.
You must be logged in to post a comment Login