Coronavirus
Coronavirus ta kama mutum 576 cikin sa’o’i 24 a Najeriya
Cibiyar dakile bazuwar cutuka ta kasa NCDC ta sanar da samun karin mutum 576 dauke da cutar Covid-19 a ranar Talata, a jihohi 21 na kasar nan, da kuma babban birnin tarayya Abuja.
A sanarwar da NCDC ta fitar a shafinta na Twitter ta ce, karin da aka samu na nufin adadin wadanda suka kamu cutar Corona a Najeriya ya kai 37,801, mutum 15,677 daga ciki an sallame su, bayan da sakamakon gwaji ya nuna cewar sun warke sarai daga cutar.
Ya zuwa yanzu NCDC ta ce, mutane 805 ne, suka rasa ransu, sanadiyyar cutar ta Corona a Najeriya.
A nan Kano ma, kididdigar gwajin cutar Corona a jihar ya nuna cewa, a ranar Talata an samu karin mutane 14 dauke da cutar, cikin mutane 865 da aka yiwa gwajin cutar.
Ma’aikatar lafiya ta Kano ta sanar a shafinta na Twitter cewar, adadin wadanda suka kamu da cutar Corona a jihar ya kai 1,430 cikin mutane 23,559 da aka yiwa gwajin cutar tun bayan bullarta a Kano.
Mutum 1,125 ne suka warke daga cutar ta Corona, sai mutum 53 da cutar ta zamo sanadiyyar ajalin su.
Yanzu haka masu cutar Corona 252 suka rage, wadanda ke ci gaba da jinya a cibiyoyin killace masu cutar dake Kano.
A jihar Kaduna kuwa, hukumomin lafiya sun tabbatar da sallamar mutum 59 da suka warke daga cutar ta Corona a ranar Talata.
Gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na Twitter cewar, sakamakon gwajin da aka yiwa mutane 108 a ranar Talatar, ya nuna cewa 20 daga ciki na dauke da cutar ta Corona.
Zuwa yanzu jihar Kaduna ce ke mataki na takwas a yawan masu cutar Corona a Najeriya wadda ke da mutane 1,211.
You must be logged in to post a comment Login