Coronavirus
CoronaWave2: Tambuwal ya killace kansa

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya killace kansa bayan bayyanar wasu alamomin cutar Corona.
A wata sanarwa da gwamnan ya fitar ya ce, wasu cikin makusantansa sun kamu da cutar a don haka ne shi ma ya killace kan sa.
Tambuwal ya nemi al’umma kan su ci gaba da bin dokokin kariya game da cutar ta Covid-19.
A cewar, Tambuwal mataimakinsa Mannir Muhammad Ɗan Iya zai ci gaba da gudanar da al’amuran gwamnati kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada.
You must be logged in to post a comment Login