Coronavirus
Covid-19: Abinda yasa ake samun “0 Case” a Kano
Tun bayan bullar cutar Covid-19 a Kano akan samu wasu ranaku da ba a samu kari na wadanda aka gano suna dauke da cutar ba.
Ko a ranar Asabar 16 ga watan Mayun da muke ciki, ba a samu ko mutum guda dake dauke da cutar ba a Kano, haka abin yake a ranar Talata 19 ga watan Mayun.
Freedom Radio ta tambayi Farfesa Isah Sadiq Abubakar shugaban sashen gwaje-gwajen cutuka masu yaduwa na jami’ar Bayero dake nan Kano, domin jin shin ko hakan yana nufin an tasamma kassara cutar a Kano?
Farfesa: “A’a ba zamuyi saurin daukar hakan ba, domin yin hakan zai zama wani ganganci, domin idan aka dauka anyi nasarar dakile wannan cuta tun yanzu to kaga mutane za ayi sake, daga mu masu yakar abin zuwa mutanen gari”
“Ganin cewa ba a samu case ba na kwana daya abune da zai faranta mana rai, amma kuma kwana daya ba komai bane a wannan yaki, har sai in an samu hakan ya dore zuwa wani lokaci, munga cewa abin ba a samun bullar cutar shine zamuyi wannan murna cewa an fara samun nasara”.
Karin labarai:
Covid-19: Ganduje ya amince a gudanar da sallar idi a Kano
Covid-19: Buhari ya tsawaita dokar kulle a Kano
Freedom: To ko a kwai mutanen da kuka yiwa gwaji a ranar Asabar din kuma aka samu basa dauke da cutar don haka ya zama “0 Case” ko yaya?
Farfesa: “To akwai dakunan gwaji guda 3 a Kano, amma na san a dakin da nake shugabanci na jami’ar Bayero ba muyi gwajin Kano ko guda daya ba a wannan rana, ban san sauran dakunan gwajin ba”
Farfesa ya cigaba da cewa “mu a wurin mu ranar munyi aikin da aka aiko mana daga jihohin Katsina da Jigawa, Jigawa sun aiko guda 600, Katsina kuma sun aiko da guda 200 to sai ranar Lahadi mukayi aikin na Kano.
Freedom: a kididdigar da kuke fitarwa ta adadin wadanda suka kamu ko suka warke a kullum, ko akwai yiwuwar ku rika fitarwa dauke da adadin wadanda kuka yiwa gwaji a kullum, acikin su ga wadanda suka kamu domin jama’a su rika rarrabewa?
Farfesa: “Eh, ya kamata dai kam, wannan tsari ne me kyau kuma kwamiti na jiha zaiyi hakan nan bada jimawa ba.
You must be logged in to post a comment Login