Labarai
COVID-19- Amurkawa dubu biyu suka rasa rayukan su
Amurkawa dubu biyu ne suka rasa rayukansu cikin kwana guda, sakamakon ci gaba da yaduwar cutar corona.
Kididdiga da jami’ar John Hopkins ta fitar, ta ce, ya zuwa karfe takwas da rabi na daren jiya laraba, alkaluman mutanen da suka mutu cikin awanni ashirin da hudu sun kai dubu biyu.
A cewar jami’ar ta John Hopkins, wannan shine rasa rayuka karo na biyu a jere mafi muni a kasar tun bayan bullar cutar ta covid-19.
Ya zuwa yanzu dai, jimillar wadanda suka mutu a kasar ta amurka sanadiyar cutar corona, ya kai dubu goma sha hudu da dari shida da casa’in da biyar; adadin da ya zarce na kasar spain wanda mutane dubu goma sha hudu da dari biyar da hamsin da biyar suka mutu.
Rahotanni sun ce, ya zuwa yanzu kasar Italiya ce ke kan gaba a yawan adadin wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar cutar ta corona, inda mutane dubu goma sha bakwai da dari shida da sittin da tara suka rasu.
You must be logged in to post a comment Login